Kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA , ya kawo cewa: an binne gawarwakin shahidai uku da suka yi shahada a harin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kai kan masu juyayin Husain a ranar Ashura a birnin Sakkwato inda aka binne su a wannan birni. An gudanar da zaman makokin Ashura na Husain As a sassa daban-daban na Najeriya tare da halartar masoyan Aba Abdullah AlHusain (AS) kuma yayin da wannan taruka anyi su a garuruwa da dama na Najeriya cikin kwanciyar hankali; sai dai 'Yan sanda a Sakkwato sun bude wuta kan Masu makokin Husain As. An yi zaman makokin Ashura a birnin Sakkwato; Amma ba a san dalilin da ya sa 'yan sandan suka bude wa mutanen wuta ba bayan taron!

27 Agusta 2021 - 13:23